Boyskido Mairamar Daura (Ruqaiya Mustapha Bukar) Скачать
Boyskido
Mairamar Daura (Ruqaiya Mustapha Bukar)
Текст песни
Beats Smith X
Boyskido
Sarauta ta zo da daraja
Haske ta sauka cikin Daura
Dole abar mata kayan ta
Muna yabon Mairamar Daura
Ga labule asirin daki
Hankaka maida dan wani naki
Mairamar Daura sha-kurumin ki
Girmin ki ne Allah ya baki
Ga labule asirin daki
Hankaka maida dan wani naki
Mairamar Daura sha-kurumin ki
Girmin ki ne Allah ya baki
Yan Daura suna kaunar ki
Yan uwa suna kewar ki
Allah ke taimaka maki
Hajiya Ruqaiya da girman ki
Yan Daura suna kaunar ki
Yan uwa suna kewar ki
Allah ke taimaka maki
Hajiya Ruqaiya da girman ki
Taka, sannu diyya ga madawakin Daura
Mun gaisheki
Marigayi Mustapha Bukar Allah ya jikan ka Sanata
Ruqaiya Mustapha Bukar mun gaida ke ne shalele
Kilishin Madawakin Daura mun gaida ke ne shalele
Kalli jikinta ta sako zinari walkiya take yi Shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Allah ya baki girma
Girman da bai misaltuwa
Mairamar Daura lallai kina da kwarjini ne ga kowa
Dan mun gani, mun sheda kina da halin dattijawa
Albishirin ku mutanen Daura kun samo mai kullawa
Da girman kujerar ki matar manya
Mairamar Daura Hajiya Ruqaiya
Kilishin Madawakin Daura
Zanyo batu a kan ta ku saurara
Ita mace ce mai kula da Sallah
Tana da tausayi kuma ga kyauta
Tana girmama wanda ya girme ta
Ta maida makiyan ta masoya
Baza a raina ki ba ai kin wuce su
In har kikai' ado wane Dawisu?
Suna maganganu amman kin share su
In dai kikai' ado wane Dawisu?
Ruqaiya Mustapha Bukar mun gaida ke ne shalele
Kilishin Madawakin Daura mun gaida ke ne shalele
Kalli jikinta ta sako zinari walkiya take Shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Gaisuwa ta ban girma ga Dr. Umar Farouk Umar Sarkin Daura
Muna alfahari da samun ka shugaban kirki
Muhammad Majidadi, miji ga Hajiya Rukayya
Makaman dokar danbam Ka fito daban dole mu gaishe ka
Hajiya Rakiya (muna gaishe ki)
Hajiya Zuwaira Bukar (muna gaishe ki)
Hajiya Hauwa (muna gaishe ki)
Alhaji Sule Majidadi (muna gaishe ka)
A gaida diyan hajiya (muna gaishe ki)
Nasreen Diyyar Hajiya (muna gaishe ki)
Ga Rahama diyyar Hajiya (muna gaishe ki)
Muna gaishe ku!
Ruqaiya Mustapha Bukar mun gaida ke ne shalele
Kilishin Madawakin Daura mun gaida ke ne shalele
Kalli jikinta ta sako zinari walkiya take Shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Ruqaiya Mustapha Bukar mun gaida ke ne shalele
Kilishin Madawakin Daura mun gaida ke ne shalele
Kalli jikinta ta sako zinari walkiya take Shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Hajiya Ruqaiya shalele
Hajiya Ruqaiya
Hajiya Ruqaiya
Beats Smith X
Треки от исполнителя