Ali Jita Mai Waka Скачать
Текст песни
Mai waka
Mai waka
Mai waka
Mai waka (Prince production)
Ga fatan mai waka
Ga lafazin mai waka
Ga zancen mai waka
Ga hujjar mai waka
Nafada na kara, wanda yaso ka kaso shi
Wanda yakika ka kyale shi
Hassada babban ciwo a zuciyar mai kullata
Nagaba tuni yayi gaba haka Allah ya hukunta
Ga zuma rumbun dadi, madaciya bamu kulata
Tsuntsu daga Allah ne, daukakarsa a duba ta
Jirgin sama yayi sama, kwanya an nunata
Sowa ta kaure gari mai fada ya shelanta
Mai waka da yake waka
Kunji azancin mai waka
Ko a ina sai mun leka
Da farin zare zamu saka
Sakon nan sai mun mika
Damu da kowa da alaka
Mai waka sai mai waka
Ga Ali Jita na waka
Ina Nazifi mai waka
Da Naziru ma sarkin waka
Umar namu yana waka
Adamu Zango mai waka
Ado Gwanja na waka
Da Usaini Danko na waka
Adamu Nagudu yana waka
Lilin Baba yana waka
Baban Chakwai mai waka
Da El'Muazu yana waka
Breaker Hamisu na waka
Nura M Inuwa waka
Lalayyo baban waka
Mahmud ko yabar waka?
Dukanmu kunga mawaka ne
Kowa yanada masoya ne
Wasu burinsu su bace mu
Wai mu yan nanaye ne
In mu yan nanaye, to kai din dan wanene?
Waka tai mana komai ne
Idan ka musa kuma kagane
Wani aikinsa siyasa ne
Wani kuma shi dan sanda ne
Wani mai tukin jirgi ne
Wani ko shi alkali ne
Wani likitan dabbobi ne
Wani likitan na mutane ne
Wani shi mai koyarwa ne
Amma wani kuma mai koyone
Siyo ka siyar aikin wani ne
Amma wasu kuma dillalai ne
Wani mai kamun kifi ne
Wannan kunga mahauci ne
Haka Allah ke ikon sa mukuma kunga mawaka ne
Hassada babbar cuta
Annabi ma yayi haninta
Kowa na harkarsa tamu wasu na damunta
Mai waka ga zakin waka
Mai waka ga jitan waka
Mai waka ga zakin waka
Mai waka ga jitan waka
Mai waka ga zakin waka
Ga jitan waka
Ga zakin waka
Ga jitan waka
Треки от исполнителя